Kudirin kasafin kudi na shekarar badi ta 2023 na naira tiriliyan 20.5 ya tsallake karatu na biyu a majalisun dattawa da ta wakilai

0 75

Kudirin kasafin kudi na shekarar badi ta 2023 na naira tiriliyan 20.5 ya tsallake karatu na biyu a majalisun dattawa da ta wakilai.

Babban zauren majalisar ya mika kudirin dokar ga kwamitinta na kasafin kudi domin ci gaba da gudanar da ayyukan majalisa tare da nuna rashin gamsuwa da karin kudaden da ake kashewa akai-akai wanda ya haura sama da naira tiriliyan 6 a bana zuwa sama da tiriliyan 8 da za a yi kasafin shekara mai zuwa.

A cewar ‘yan majalisar, Najeriya ba za ta iya ci gaba da karbar bashi domin samun kashi 1 na al’ummarta ba. Daga bisani, majalisar dattawa ta bukaci kwamitinta da ya dawo da rahoto nan da makonni hudu.

Ta dage zamanta na tsawon makonni hudu masu zuwa domin baiwa kwamitocinta daban-daban damar yin aiki da kididdigar kasafin kudin shekarar 2023 da kuma kare kasafin kudi na ma’aikatu da sassa da hukumomi daban-daban.

Majalisar dattawa za ta sake zama ranar 15 ga watan Nuwamba akan batun.

Leave a Reply

%d bloggers like this: