Gwamnatin Tarayya ta ce Kimanin mutane 500 ne suka mutu a sanadiyar ambaliyar ruwa a Najeriya

0 98

Gwamnatin Tarayya ta ce Kimanin mutane 500 ne suka mutu a sanadiyar ambaliyar ruwa a sassan kasar nan.

A cewarta, kawo yanzu Jihohi 31 ne ciki harda birnin tarayya Abuja ne ambaliyar ta shafa, tare da raba mutane Miliyan 1 da dubu 400 da muhallansu.

Gwamnatin ta ce ambaliyar ta lalata gonakai tare da rushe Gidaje a sassan kasar nan ciki harda birnin tarayya Abuja.

Haka kuma ta ce bazata iya yin hasashen asarar da ambaliyar ruwan ta yiwa tattalin arzikin kasa ba zuwa yanzu.

Babban Sakatare a Ma’aikatar Jinkai, Iftila’in da Cigaban Al’umma Dr Nasir Sani Gwarzo, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake bada ba’asin yadda ambaliyar ta shafi sassan kasar nan.

Haka kuma ya ce sabon Daftarin Kudurin Bada Agajin Gaggawa na Kasa, wanda Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince da shi zai taimakawa masu ruwa da tsaki wajen tantance ta’adin da ambaliyar ruwan ta yi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: