Wasu sojojin Najeriya sun kashe wani fitaccen jagoran ‘yan bindiga a jihar Kaduna da mayakansa 30

0 107

Jaridar PRNigeria ta ce sojojin Najeriya sun kashe wani fitaccen jagoran ‘yan bindiga a jihar Kaduna, Ali Dogo da mayakansa 30.

An bayyana cewa, an kashe Mista Dogo, wanda aka fi sani da Yellow, tare da ‘yan kungiyarsa, sakamakon harin da jiragen yakin rundunar sojin sama ta Operation WHIRL Punch suka kai a karshen mako.

Yayin da yake tabbatar da kisan Yellow da mayakansa, wata majiyar leken asiri ta tsaro ta shaida wa PRNigeria cewa fitaccen shugaban ‘yan fashin, da ‘yan ta’addansa sun gudu daga jihar Neja zuwa wani gidan Alhaji Gwarzo da ke Yadi a karamar hukumar Giwa domin tsira da rayukansu.

Biyo bayan harin bama-bamai da jiragen yakin sojojin saman Najeriya suka kai a yankin.

A halin da ake ciki kuma, PRNigeria ta kuma gano cewa an kai hare-haren bama-bamai a rana guda kan ‘yan ta’adda a wani wuri mai nisan kilomita 33 Arewa maso yammacin Mando a Kaduna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: