Sanata Kabiru Gaya ya ce jam’iyyar NNPP ba za ta zama barazana ga ‘yan takarar jam’iyyar APC a zaben 2023 ba

0 50

Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya ce jam’iyyar NNPP ba za ta zama barazana ga ‘yan takarar jam’iyyar APC a zaben 2023 a jihar Kano ba.

Gaya, wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar dattijai kan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ya bayyana haka ne a yayin wata tattaunawa da manema labarai a gidansa da ke Kano jiya da yamma.

Ko da yake ya amince cewa babban abokin hamayyarsa dake neman kujerar Kano ta Kudu, Kawu Sumaila na jam’iyyar NNPP yana jan hankalin jama’a.

Amma ya tabbatar da cewa yana da kwarin gwiwar komawa majalisar dattawa karo na biyar.

Kabiru Gaya ya kuma zayyana wasu daga ayyukan daya gudanar da suka hada da tona burtsatse sama da 919, ajuzuzuwa 600 da kuma gyaran wasu hanyoyi da dama.

Ya kuma dauki nauyin dalibai 16 da sukeyin karatu a kasashen waje, ya taba motoci sama da 600, da kuma babura sama da 1000 da dai sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: