Kungiyar Likitoci: An tilasta mana janyewa amma yajin aiki ba gudu ba ja da baya

0 99

Kungiyar likitocin Najeriya ta sha alwashin ci gaba da yajin aikin har sai baba ta gani, duk kuwa da yarjejeniyar da suka rattabawa hannu da gwamnatin tarayya na janye wa’adin shiga yajin aikin.

A jiya Alhamis ne kungiyar likitocin ta shiga yajin aikin na gama-gari a kasar, saboda “kasawar da gwamnati ta yi na biyan bukatunsu, ciki har da biyan albashi da likitocin ke bin gwamnati bashi.

Yajin aikin ya zo ne kwana daya bayan da gwamnati ta yi yunkurin hana likitocin shiga yajin aiki, ta hanyar tattaunawa da su da kuma rattaba hannu akan wata yarjejeniya ta janye shirin shiga yajin aikin a ranar Larabar da ta gabata.

To sai dai kungiyar ta ce an tilasta mata sa hannu a yarjejeniyar ne ba bisa son ran ta ba a lokacin taron na bangaren gwamnati da shugabannin kungiyar, wanda aka gudanar a ofishin Ministan kwadago Chris Ngige.

Ministan Kwadagon Najeriya Chirs Ngige
Ministan Kwadagon Najeriya Chirs Ngige

Kungiyar likitocin a shafinta na twitter, ta baiwa ‘yan Najeriya hakuri, tare da neman su fahimci yanayin da suke ciki, tana mai bayyana cewa ba ta shiga yajin aikin ne domin kuntatawa ‘yan kasar ba, sai dai domin matsawa gwamnati lambar kara azama wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na kula da lafiyar jama’a.

Da yake tabbatar da soma yajin aikin, shugaban kungiyar likitocin Dr. Uyilawa Okhuaihesuyi, ya ce sun gaji da sa hannu akan yarjejeniyoyi da gwamnatin tarayya amma ba’a aiwatarwa, inda ya ce har kawo yanzu ba’a taba aiwatar da wata yarjejeniya ko daya da suka kulla da gwamnati a cikin shekaru 10 da suka gabata ba.

Dr. Uyilawa Okhuaihesuyi, Shugaban Kungiyar Likitocin Najeriya
Dr. Uyilawa Okhuaihesuyi, Shugaban Kungiyar Likitocin Najeriya

Ko baya ga neman biyan albashin da likitoci ke bin gwamnati bashi, kungiyar na kuma bukatar gwamnati da ta kara yawan kudin alawus na hatsarin ma’aikatan kiwon lafiya da sauran hakkokin barazanar yaki da cutar COVID-19 da suke fuskanta a asibitoci.

Haka kuma suna neman a rage yawan kudaden da membobinsu ke biya na samun horo na waje a dukkan manyan manyan makarantun kasar ba tare da wani jinkiri ba.

Yajin aikin na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya yi balaguro zuwa birnin London domin duba lafiyarsa.

https://www.voahausa.com/a/yajin-aiki-ba-gudu-ba-ja-da-baya-duk-da-an-tilasta-mana-janyewa—kungiyar-likitocin-najeriya/5838116.html

Leave a Reply

%d bloggers like this: