Kungiyar masu biredi ta Najeriya ta umarci duka mambobinta da su kara farashin kayansu da kashi 30

0 229

Kungiyar masu biredi ta Najeriya ta umarci duka mambobinta da su kara farashin kayansu da kashi 30 cikin 100 saboda karuwar farashin sinadaren hada biredi da dangoginsa.

Umarnin na zuwa ne bayan da aka cimma matsayar a karshen tattaunawar majalisar zartarwar kungiyar da aka yi a Abuja.

Da yake bayani kan dalilan kara farashin shugaban kungiyar na kasa Mansur Umar, ya ce karuwar farashin Siga da bota da filawa duka na cikin abubuwan da suka janyo daukar wannan matakin nasu.

Lokacin da yake yaba wa gwamnatin tarayya kan daidaita shirinta na yin filawa da makani, shugaban ya ce farashin filawar da suke siya a kasa da naira miliyan shida da a duk mota guda yanzu suna sayanta kan naiara miliyan 9.Article share tools

Leave a Reply

%d bloggers like this: