Kungiyar masu gudanar da dakunan karatu ta kasa reshen jihar Jigawa ta zabi sabbin shugabannin ta

0 115

Kungiyar masu gudanar da dakunan karatu ta kasa reshen jihar Jigawa ta zabi sabbin shugabannin ta, da zasu jagoranci kungiyar na tsawon shekaru uku.

Wadanda aka zaba sun hada da Honorabul Sagir Musa Ahmed, kwamishinan kasa da gidaje a matsayin shugaba, da Danladi Yusuf na Binyaminu Usman Polytechnic Hadejia a matsayin mataimakin shugaba, sai Adamu Sa’ad Madaki na Jami’ar Tarayya dake Dutse a matsayin sakatare da Magaji Danjummai na Kwalejin Ilimi da Nazarin Shari’a dake Ringim a matsayin Mataimakin Sakatare.

Sauran su ne Baba Abdu na Jami’ar Sule Lamido, Kafin Hausa a matsayin Ma’aji, da Abdullahi Abubakar mai wakiltar Makarantun Kiwon Lafiya na Jiha a matsayin sakataren kudi da Gambo Kwara na Kwalejin Ilimi ta Jihar Jigawa dake Gumel a matsayin jami’in hulda da jama’a.

Hakan yazo ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren kungiyar, Adamu Sa’ad Madaki, wacce mataimakin shugaban kungiyar, Malam Danladi Yusuf ya aikowa Sawaba.

Sanarwar ta kara da cewa taron masu ruwa da tsaki na gaba na kungiyar zai gudana a makarantar Informatics dake Kazaure.

Leave a Reply

%d bloggers like this: