NEMA ta fara rarraba kayan aikin gona ga manoma dubu 6 da 573 da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Yobe

0 91

Shirin Tallafin Noma na Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ya fara rarraba kayan aikin gona ga manoma dubu 6 da 573 da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Yobe.

Babban Jami’in Yada Labarai na Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa, shiyyar Arewa maso Gabas, Abdulkadir Ibrahim, ya bayyana haka yau a Damaturu, babban birnin jihar.

Abdulkadir Ibrahim ya ce aikin rabon yana karkashin Asusun Agajin Gaggawa na Gwamnatin Tarayya ga manoman da ambaliyar ruwa ta shafa a bara a jihar Yobe, tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar da sauran masu ruwa da tsaki.

A nata jawabin, Shugabar Shirin Tallafin Noma na Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa a jihar Yobe, Wagami Lydia, ta ce rabon tallafin zai bunkasa samar da abinci a fadin jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: