Kungiyar Matasan Arewa Masu Bada Shawara ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin BBNaija

0 170

Kungiyar Matasan Arewa Masu Bada Shawara, ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin Big Brother Naija wanda akafi sani da BBNaija, wanda ake haskawa a gidan Talabijin.

Shugaban Kungiyar na Kasa Yerima Shettima, shine ya bayyana hakan, inda ya kara da cewa, shine ya zama tamkar wata annoba a kasa.

Comrade Yerima Shettima, ya ce shirin yana nuna shirye-shiryen batsa, wanda yake ruguza tarbiya.

Shugaban Kungiyar ya bukaci yan Najeriya masu kishin kasar nan, su fito su nunawa gwamnati irin illolin da shirin yake dashi ga zaman takewa.

Gidan Talabijin na BBNaija yana yada shirye-shiryen sa a wani gida da aka ware, inda kuma ake dora kudade masu tarin yawa, kan wanda suka samu nasara daga cikin yan wasan a matsayin gudunmawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: