Kusan kashi biyu bisa uku na dukkan yaran Ukraine sun tsere daga gidajensu cikin makonni shida tun bayan mamayar Rasha

0 32

Kusan kashi biyu bisa uku na dukkan yaran Ukraine sun tsere daga gidajensu cikin makonni shida tun bayan mamayar Rasha.

Hakan na zuwa ne a wata sanarwa da hukumar kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta fitar jiya.

Majalisar Dinkin Duniya ta kuma tabbatar da mutuwar yara 142, duk da ta yi gargadin cewa adadin zai iya fin haka sosai.

Daraktan shirye-shiryen gaggawa na hukumar UNICEF, Manuel Fontaine, wanda ya dawo daga Ukraine, ya ce samun yara miliyan 4.8 daga cikin yara miliyan 7.5 na kasar Ukraine da suka rasa matsugunansu cikin kankanin lokaci, inda yace  wani abu ne da bai taba ganin ya faru ba cikin gaggawa, cikin shekaru 31 na ayyukan jin kai.

A halin da ake ciki, jakadan Majalisar Dinkin Duniya na Ukraine ya yi ikirarin cewa Rasha ta kwashe yara fiye da dubu 121 daga Ukraine kuma an bayar da rahoton cewa ta tsara daftarin doka don saukakawa da kuma hanzarta hanyoyin daukar nauyin kula da yara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: