Kwamatin Kula da Ciniki da Masana’antu na Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ya yaba da kasafin kuɗin shekara mai zuwa

0 145

Kwamatin Kula da Ciniki da Masana’antu na Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ya bayyana gamsuwa dangane da bunkasar samar da ayyukan yi da harkokin zuba Jari da yake kunshe cikin kudirin kasafin kudi na shekara ta 2022 na gwamnatin jiha.

Shugaban Kwamatin Alhaji Muhammad Sa’idu Abubakar, shine ya bayyana hakan lokacin da yake tantance kiyasin kasafin kudin ma’aikatar ciniki da masana’antu na sabuwar shekara a zauren majalisar.

Ya lura cewa kudirin gwamnatin jiha na bunkasa harkokin kasuwanci a manyan kasuwannin jihar nan zai bunkasa tattalin arziki da jindadin al’ummar jihar nan.

Shugaban Kwamatin ya kuma bayyana farin cikinsa bisa tsarin gwamnati na samar da tallafin cutar Corona ga kananan da kuma matsakaitan yan kasuwa ta hanyar samar da rance daga bakin duniya ta hannun gwamnatin tarayya.

A nasa jawabin Kwamishinan Ma’aikatar Ciniki da Masana’antu Alhaji Salisu Zakar, ya bayyana cewa ma’aikatar ta kiyasta kashe Naira Biliyan 2 da Miliyan 57 wajen gudanar da manyan ayyuka da kuma na ayyukan yau da kullum a sabuwar shekara mai zuwa.

Ya ce bangarorin da Ma’aikatar tafi baiwa fifiko a sabuwar shekara su ne bayar da tallafi ga Kananan da Matsakaitan yan Kasuwa, da kafa masana’antu a yankin da aka ware don gina masana’atu na Gagarawa da kuma manyan Kasuwanni da suka hadar da Kasuwar Duniya ta Maigatari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: