Kwamatin Sauraron Korafe-Korafen tarukan zaben Shugabannin Jam’iyar APC na Jihohi da ake gudanar mai mutane 5 ya isa Kano.

Manema Labarai sun rawaito cewa an gudanar da zaben shugabannin Jam’iyar a bangare biyu a kuma wurare daban-daban, inda aka zabi Dr Abdullahi Abbas a bangaren gwamnati da kuma Ahmadu Haruna Danzago a bangaren Malam Ibrahim Shekarau.

Shugaban Kwamatin Mai mutane 5 wanda Ofishin Jam’iyar na Kasa ya turo Mista Tony Macfoy, ya ce zai saurari korafin zaben da aka gudanar a filin taro na Sani Abasha ne kawai.

A cewarsa, Uwar Jam’iyar ce ta kasa ta turoshi domin saurarorin korafin masu ikirarin ba’a musu Aladalci ba, inda ya kara da cewa zai saurari korafin wadanda suka umarci ya saurari nasu ne kawai.

Kazalika, ya ce Kwamitinsa zai zauna a jihar tsawon kwanaki 3 wanda suka hada da yau Asabar zuwa Litinin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: