Kwamishinan ilimi Kimiyya da fasaha na jihar Jigawa, Dakta Lawan Yunusa Danzomo ya kaddamar da wakilan kwamitin da zasu ziyarci manyan makarantun gaba da sikandire na jihar nan domin ganin halin da suke ciki tare da gabatarwa da gwamnati rohoto.

A jawabinsa lokacin bikin kaddamarwar kwamishinan ya ce makasudin kafa kwamatin shi ne shigar da masana cikin harkokin ilimi domin su bada gudunmawarsu, inda ya ce an zabi wakilan kwamatin ne bisa cancanta.

Dakta Lawan Yunusa Danzomo ya ce daga cikin ayyukan da yan kwamatin zasu duba a lokacin ziyarar makarantun sun hadar da tsarin shugabanci da gudunmawar da majalisar gudanarwar makarantun suke yi da kuma duba ayyukan manyan jami’an makarantun.

Haka kuma ya ce ana sa ran yan kwamatin zasu duba yanayin koyo da koyarwar makarantun ciki har da abubuwan more rayuwa da ayyukan malaman makarantun da kuma yadda suke gudanar da harkokin jarrabawa baya ga lura da tsarin cigaban ma’aikatan makarantun tare da gabatar da shawarwarin da zasu inganta harkokin koyo da koyarwa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: