Masu dafa abinci ta cikin shirin gwamnatin tarayya sunce matsalar basu kudaden dafa abincin yana shafar zuwan dalibai makaranta

0 101

Mata Masu Dafa Abinci ta cikin shirin gwamnatin tarayya na Ciyar da Dalibai yan Makaranta sun bayyana cewa tsaikon da ake samu wajen basu kudaden dafa Abincin yana shafar zuwan Daliban Makaranta.

Wata Mata wanda take cikin Matan da suke dafa abincin ce ta bayyana hakan ga Manema Labarai a Duste a lokacin da ake mika musu kwanikan zubawa Daliban Abinci.

A cewarta, gwamnatin tarayya ta kirkiri shirin ne domin ta kara yawan adadin daliban da suke zuwa makaranta tare da kuma samarwa matan abinyi.

Matar da shawarci gwamnatin tarayya ta rika biyan masu dafa abincin da wuri, matukar tana son shirin ya kai ga nasara.

A Jabawabin ta, Ministar Ma’aikatar Jinkai, Iftila’i da Cigaban Al’umma Hajiya Sadiya Umar Farouk, ta ce kimanin Dalibai miliyan 9 ake ciyarwa a kasar nan, tare da daukar masu dafa Abinci su dubu 10,000.

Leave a Reply

%d bloggers like this: