Laftanal Janar Farouk Yahaya ya bayyana damuwa dangane da cin zarafin mata a barikokin soji

0 160

Babban hafsan sojin kasa na kasa Laftanal Janar Farouk Yahaya a yau ya bayyana damuwa dangane da karuwar korafe-korafen cin zarafin mata a barikokin soji dake fadin kasarnan.

Faruk Yahaya, wanda ya samu wakilcin kwamandan makarantar kere-kere ta sojin Najeriya, Birigediya Janar Mark Mamman, ya dora alhakin matsalar akan rashin zaman sojoji a gidajensu, inda yace a koda yaushe basa tare da iyalansu.

Yayi jawabi a wajen taron sojin Najeriya mabiya darikar katolika na bana da ake gudanarwa a Makurdin jihar Benue.

Ya nanata cewa babbar matsalar cin zarafin kananan yara shine zata iya haifar da matsalolin da cin zarafin ke jawowa, wadanda a halin yanzu ake fuskanta a yakin da da ake yi da ta’addanci a Arewa maso Gabas.

Leave a Reply

%d bloggers like this: