Sule Lamido yace yana da kwarin gwiwar cewa jam’iyyarsa za ta kafa gwamnati a 2023

0 527

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Dr. Sule Lamido, yace yana da kwarin gwiwar cewa jam’iyyarsa za ta kafa gwamnati bayan zaben gama gari na shekarar 2023.

Sai dai, yace jam’iyyar tana iya kasa aiwatar da abubuwan alkhairi fiye da jam’iyyar APC.

Sule Lamido, wanda ya sanar da haka yayin zantawa da manema labarai, yace jam’iyyar APC ta tabbatarwa da ‘yan Najeriya cewa ta gaza saboda kasawarta wajen cika alkawarukan neman zabe.

Ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam’iyyar PDP za ta dawo mulki a shekarar 2023.

Yace jam’iyyar APC mai mulki za ta ruguje kafin zaben 2023 saboda ginshikan da aka kafata akai zasu rushe baki daya.

Leave a Reply