‘Yan Sanda na cigaba da farautar mutanen da suka yiwa wata yarinya kuma dalibar kakarantar firamaren fyade a Hadejia

0 82

Rundunar yan Sandan Jihar Jigawa na cigaba da farautar mutanen da suka yiwa wata yarinya kuma Dalibar Makarantar Firamaren fyade a nan karamar hukumar Hadejia.

Kakakin Rundunar ASP Lawan Shiisu Adam, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Dutse.

A cewarsa a ranar likitin ne rundunar ta samu rahoton wasu mutane sun yiwa wata yarinya yar shekara 10 fyade a Makarantar Firamare ta Dallah dake nan Hadejia.

SP Shiisu Adam, ya ce mutanen sun yiwa yarinyar fyade a tare da ji mata raunika, inda kuma suka tsere.

Haka kuma ya ce bayan faruwar lamarin ne aka dauki yarinyar zuwa Babban Asibitin Hadejia domin duba lafiyarta, tare da kwantar da ita a Asibitin.

Kazalika ya ce rundunar tana aiki domin kamo mutanen da ake zargi da aikata laifin domin hukunta su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: