An nada DCP Tunji Disu a matsayin sabon Shugaban Tawagar Tattara Bayanan Sirri wanda ya maye gurbin Abba Kyari

0 70

An nada Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda, DCP Tunji Disu a matsayin sabon Shugaban Tawagar Tattara Bayanan Sirri ta Police Intelligence Response Team (IRT).

Matakin na ranar Litinin na zuwa ne bayan amincewar Babban Sufeton ’Yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba.

Kazalika, matakin na zuwa ne biyo bayan dakatarwar da aka yi wa DCP Abba Kyari daga aikin dan sanda a ranar Lahadi sakamakon tuhumar da Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Kasar Amurka FBI ke yi masa na karbar cin hanci.

A Lahadin da ta gabata ce Hukumar Kula da Aikin Dan sanda a Najeriya ta dakatar da Abba Kyari daga aikin dan sanda sakamakon zargin hannun a wata damfara da Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka ta FBI ke yi masa.

Cikin sanarwar da Jami’in Hulda da Al’umma na rundunar Frank Mba ya fitar, ya ce nadin DCP Disu zai fara aiki nan take, inda Babban Sufeton ke shawartarsa da ya kasance kwararre a kan aikinsa.

Kafin nadin nasa DCP Tunji Disu, ya taba zama shugaban tawagar kaiwa agajin gaggawa na rundunar yan sanda a jihar Lagos, haka kuma ya taba zama mataimakin kwamishinan a sashen gudanarwa na Ofishin hukumar tsaro ta yan sandan kasa.

Tunji Disu, ya samu shaidar Digiri kan Turanci a Jami’ar Lagos, haka kuma ya yi digiri na biyu a kan fannin mulki a jami’ar Adekunle Ajasin ta jihar Ondo.

Leave a Reply

%d bloggers like this: