Majalisar wakilan Nijeriya ta ce tana yin nazari domin soke shirin nan na bauta wa kasa wato NYSC da aka fara kusan shekaru arba’in da takwas bayan kafuwarta ta lokacin mulkin soja na Janar Yakubu Gowon a ƙasar.

Majiyar DCL Hausa tace tuni majalisar ta bayyana cewa ta shirya yi wa kudirin soke hidimta wa kasar da dan majalisa Awaji-Inombek Abiante mai wakiltar mazabar Andoni-Opobo/Nkoro na jihar Rivers ya kawo mata karatu a zauren majalisar.

Awaji-Inombek Abiante, wanda ya kawo kudirin ya bayyana dalilansa da suka sa za a yi la’akari da soke shirin a cikin wani bayanin sa ya yi wa majalisar game da sha’awar shi ta yin hakan.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: