Majalisar dattawa ta bibiyi kudirin gyaran dokar zabe kuma ta hana zaben ta kafar itanet

0 80

A wani cigaban kuma, majalisar dattawa ta bibiyi kudirin gyaran dokar zabe domin zartarwa.

Sai dai,an samu katsen aikin sanadiyyar jayayya tsakanin yan majalisar, bisa sashe na 52, karamin sashe na 3 na kudirin.

Sashen yana magana ne akan aikawa da sakamakon zabe ta internet, a lokacin zabe.

Sashen ya bayyana cewa hukumar zabe zata iya aikawa da sakamakon zabe ta internet idan da hali.

Sanatocin na bibiyar sashe bayan sashe na kudirin a lokacin da suka zo wannan sashen kuma mataimakin bulaliyar majalisar, Sabi Abdullahi, yayi kokarin gyaran sashen.

Hakan ya jawo cece-kuce a zauren majalisar amma sai shugaban majalisar, Sanata Ahmad Lawan, yace a kada kuri’a akan gyaran.

Da aka kada kuri’a, wadanda suka ki amincewa a gyara sun rinjayi wadanda suka goyi bayan gyaran amma Ahmad Lawan ya yanke hukuncin gyarawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: