Labarai

Majalisar Dattawa ta kara wa’adin kammala aiwatar da kasafin kudin badi daga ranar 31 ga watan Maris zuwa 31 ga watan Mayu

Majalisar Dattawa ta kara wa’adin kammala aiwatar da kasafin kudin badi daga ranar 31 ga watan Maris zuwa 31 ga watan Mayu.

Hakan ya biyo bayan amincewa da wani kudiri na neman gyaran dokar kasafin kudin na 2021.

Majalisar ta dattawa kafin amincewa da kudirin, sai da ta dakatar da doka ta 78 a cikin dokokin majalisar dattawa, wanda ya bata damar sauya ranakun aiwatar da kasafin kudin.

An karanta kudirin a yau yayin zaman majalisar, a karatu na farko, biyu da na uku.

Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Yahaya Abdullahi ne ya dauki nauyin kudirin.

Da yake jagorantar mahawara akan kasafin kudin, Yahaya Abdullahi yace an zartar da dokar kasafin kudin a tsakiyar shekara, kamar yadda aka saba, inda aka dage aiwatar da kasafin kudin zuwa shekarar gaba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: