Babban bankin kasa (CBN) ya shawarci ‘yan Najeriya da su kauracewa kamfanonin hada-hadar kudaden da basu da rijista domin samun riba idan aka saka jari

0 61

Babban bankin kasa (CBN) ya shawarci ‘yan Najeriya da su kauracewa kamfanonin hada-hadar kudaden da basu da rijista wadanda ke dadin baka na samun riba idan aka saka jari.

‘Yan Najeriya da dama sun fada komar irin wadannan kamfanonin wadanda ke alkawarin bayar da riba har kashi 100 bayan saka jari.

Kamfanonin, wadanda yawanci suke internet basu da ofis a zahiri, suna bacewa bayan sun karbi kudade dayawa daga wajen daruruwan mutane.

Hukumomin da abin ya shafa sun kama wasu daga cikin wadanda ke gudanar da irin wadannan kamfanonin.

Babban bankin kasa (CBN) ta karkashin kwamitin sanya ido kan hada-hadar kudade, ya shawarci ‘yan Najeriya da su dena mu’amala da irin wadannan kamfanonin.

Cikin wata sanarwa da ya wallafa jiya a shafinsa na internet, babban bankin kasa yace haramtattun kamfanonin hada-hadar kudaden na damfarar jama’a ta hanyar yi musu alkawarin karya na basu riba mai yawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: