Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta rage fiye da Naira biliyan 25 daga cikin kasafin kudin jihar na shekarar 2021

0 74

Mambobin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara sun rage Naira Biliyan 25 da Miliyan 203 da Dubu 851 daga cikin Kasafin Kudin Jihar na shekarar 2021.

Kimanin Naira Biliyan 142 da Miliyan 779 da dubu 251 ne Gwamnan Jihar ya sanyawa hannu a kasafin kudin Jihar na wannan shekara, amma Majalisar ta rage, inda ta bayar dashi zuwa Naira Biliyan 117 da Miliyan 575 da dubu 400, saboda yadda aka samu gibi a fannin tara kudaden Harajin Cikin Gida, sakamakon hare-haren yan bindiga da cutar Corona.

Yan Majalisar sun amince da rage kudaden ne bayan yin la’akari da rahoton Kwamatin Kudade na Majalisar wanda ya bukaci hakan domin sake yin Nazari.

Da yake gabatar da rahoton sa ga Majalisar Mukaddashin Shugaban Kwamatin Kudade na Majalisar Hon Shamsuddeen Hassan, ya ce matsalar tsaro wanda ta shafe sama da shekaru na daya daga cikin abubuwan da suka shafi hanyar tara kudaden shiga ga Jihar.

A nasa bangaren Kakakin Majalisar Rt Hon Nasiru Magarya, ya yabawa Kwamatin bisa yadda ya aiwatar da ayyukan sa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: