An kashe kwamandan Kungiyar Taliban a lokacin da dakarun sa suke musayar wuta da yan kungiyar ISK

0 60

An Kashe Kwamandan Kungiyar Taliban a lokacin da dakarun sa domin musayar wuta da Kungiyar ISK, bayan wani harin kunar bakin wake da aka kai wani Asibiti a birnin Kabul na Kasar Afghanistan.

Kimanin shekaru 20 kungiyar Taliban ta dauka tana yaki da gwamnatin Afghanistan wanda take da goyan bayan Amurka, kafin daga baya Taliban su karbe iko da birnin Kabul a watan Agustan da ya gabata.

Kungiyar Taliban na cigaba da samun tashin hankali daga kungiyar Islamic State Khorasan (ISK) wanda take adawa da Taliban a lokacin da ita kuma take kokarin daidaita lamura a kasar.

Kimanin mutane 19 ne aka kashe a hari na Asibitin birnin Kabul, a cewar wani Ma’aikacin Lafiya, wanda ya bukaci a sakaya sunansa.

Mista Hamdullah Mokhlis, shine babban Kwamandan Haqqani wanda aka taba kashewa tun bayan da Taliban ta karbe ikon kasar ta Afghanistan.

Kakakin Taliban Zabiullah Mujahid, ya karya adadin mutanen da ake cewa yan kashe, inda kuma ya kara da cewa an dakile harin cikin mintuna 15 da kaiwa harin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: