Wasu da ake kyautata zaton yan Daba ne sun farmaki Sanata Danjuma Goje, sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya.

An rawaito cewa an farkami Motar Sanatan ne da muggan Makami a yau, a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa birnin Gombe.

Cikin wata sanarwa da kakakinsa Mista Lilian Nworie, ya fitar kuma aka rabawa manema labarai, ya ce an farmaki Sanata Danjuma Goje ne a lokacin da yake ziyarar aiki, inda yan dabar sukayi kokarin hanashi zuwa cikin gari.

Kakakin nasa, ya ce lamarin ya faru ne a kusa da Cibiyar Taro ta Duniya wanda take kan hanyar Bauchi zuwa Gombe.

Haka kuma Mai taimaka masan, ya ce zargin cewa wadanda suka kaiwa Sanatan hari, magoya bayan Gwamna Inuwa Yahaya ne na Jihar, inda ya kara da cewa lokacin da lamarin ya faru Jami’an tsaro suna kallo amma suka ki daukar matakan da suka kamata domin hana faruwar lamarin.

Alaka tayi tsanani tsakanin Gwamna Inuwa Yahaya da Sanata Danjuma Goje, saboda rikicin Siyasa a Jam’iyar su ta APC da kuma sauran batutuwa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: