Majalisar zartarwa ta ta amince da Naira biliyan 2.5 don siyan motocin aiki ga hukumar kiyaye haddura ta kasa

0 77

Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da Naira biliyan 2.5 don siyan motocin aiki ga hukumar kiyaye haddura ta kasa.

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Femi Adesina ne ya bayyana haka a lokacin da yake yiwa manema labarai na fadar shugaban kasa bayanin sakamakon zaman majalisar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a ranar Laraba a Abuja.

An bayar da kwangilar sayen motocin ga Dangote Peugeot Automobile Nigeria Limited da Mikaino International Limited.

Da yake jawabi ga manema labarai kan sakamakon taron, Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya bayyana cewa majalisar ta amince da Naira biliyan 8 domin aiwatar da kwangiloli uku na ma’aikatar.

Ya kuma bayyana cewa majalisar ta kuma amince da siyan motocin daukar marasa lafiya guda 18 ga wasu makarantun hadin kai a shiyyoyi shida na siyasar kasar nan.

Motocin daukar marasa lafiya 18 za a sanya musu kayan aikin jinya.

Ya kara da cewa makarantun hadaka sama da 100 an zabi uku daga kowacce shiyya domin basu motocin

Leave a Reply

%d bloggers like this: