Shugaba Buhari ya ware naira bilyan 134.7 domin biyan kudin tallafin tsaro ga tsoffin sojojin Najeriya

0 90

Shugaban kasa Muhamamdu Buhari ya ware naira bilyan 134.7 domin biyan kudin tallafin tsaro ga tsoffin sojojin kasar nan

Shugaba buhari ya bayyana haka a bikin tunawa da yan mazan jiya, ya sanar da baya gudunmawa ta bilyan goma ga sojojin, a madadin gwamnatin tarayya

Kazalika shuga

Shugaba Buhari ya yi alkawarin cewa gwamnatin tarayya na tabbatar da jin dadin tsofaffin sojoji ta hanyar tabbatar da biyan su kudaden fansho da sauran hakkokinsu cikin gaggawa, ta hanyar amincewa da biyan kudaden da aka yi wa tsofaffin jami’an tsaro daga shekarar 2017.

Shugaba Buhari ya kuma bayyana jin dadinsa ta yadda hukumat kula da lafiyar tsoffin sojoji ke tafiyar da harkoki yadda ya kamata wajen samar da ayyukan kiwon lafiya ga tsofaffin sojoji, inda ya yi nuni da yadda aka fadada ayyukansu ta hanyar kafa ofisoshin shiyya da na Jiha.

Ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta ci gaba da ba da fifiko wajen samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga tsofaffi da ‘yan kasa baki daya.

Ya kuma tabbatar wa da ‘yan Najeriya cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da mayar da martani tare da karfafa dukkanin hukumomin tsaro domin su samu galaba a kan kalubalen tsaro a kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: