Majalissa Ta Amince Da Ciyo Bashin $1Bn Domin Gina Layin Dogo Zuwa Kano

0 86

Majalisar dattawan ta amince wa Bankin raya kasa na China ya samar da kuɗaɗen da za a yi amfani da su wajen gina layin dogo, wanda zai ci kusan dala biliyan ɗaya.
Tun farko, an shirya da wata cibiyar samar da rance a China, don samar da kuɗin da za a yi amfani da shi wajen gina layin dogo daga Kaduna zuwa Kano – birni mafi girma da bunƙasar kasuwanci a arewa – amma sai cibiyar ta janye daga yarjejeniyar a 2020.
Lokacin da ya hau mulki shekaru takwas da suka gabata, Shugaba Buhari ya ba da fifiko wajen inganta hanyoyin sufuri da inganta ayyukan samar da wutar lantarki.
Duk da haka, samar da kuɗaɗe ya kasance babban cikas wajen gudanar da ayyukan.
Majalisar ta amince a ciyo bashin biliyoyin dala daga China da sauran masu ba da rance na ƙasashen duniya, amma har yanzu kuɗaɗen ba su samu ba.
A lokacin da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu zai hau karagar mulki a watan Mayu, zai gaji tarin ƙalubale da suka haɗa da hauhawar farashi da taɓarɓarewar tsaro da ƙasar ke fama da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: