Za’a Kammala Aikin Hanyar Legas Zuwa Ibadan Nan Bada Jimawa Ba

0 77

Ministan ayyuka da gida Babatunde Fashola yace aikin babbar hanyar Legas zuwa Ibadan za’a kammala shi nan ba da jiwa ba, tare da kaddamar da gadar Neja da kuma budewa ababen hawa a watan Mayu.
Cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar Blessing Lere-Adams ya fitar, yace ministan ya fada hakan ne yayin da yake duba gadar jihar Nasarawa.
Sanarwar tace aikin Babbar hanyar Legas zuwa Ibadan an tsara za’a kammala shi a watan Afrilun wannan shekarar, sannan kuma za’a kaddamar da gadar Neja ta biyu a watan Mayu wannan shekarar tare da bude ta ga ababen hawa.
Ministan yace aikin gadar Loko zuwa Oweta wanda ya ratsa ta jihar Benue zai hade da yankin kudinci da yammacin kasar nan,ya kuma kara da cewa dagar zata rage cin lokaci ga matafiya,tare da rage yawan kudin sufuri da kuma bunkasa Kasuwanci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: