Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Hukumar Bunkasa Kasuwacin Zamani.

0 78

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da hukumar bunkasa Kasuwanci ta zamani.
An kaddamar da hukumar ne yayin zaman majalisar zartarwa ta kasa a yau.
Hukumar ta NCDIE,wanda shugaban kasa zai jagoranta nada mambobi 13 ciki hadda mataimakin shugaban kasa, Ministan kasafin kudi da tsare-tsare,da hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta zamani, da gwamnan babban bankin kasa CBN da sauran su.
Hukumar zata yi aiki domin bunkasa zamanin Kasuwanci da samar da damarmakin Kasuwanci a kasar nan.
Yayin kaddamar da hukumar, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi karin haske kan muhimmancin sabuwar hukumar wajen bada gudunwa a cigaban tattalin arziki da samar da ayyukan yi ga yan kasa.
Shugaba Buhari yace manufar samar da hukumar shine samar da cigaba ga kanana da matsakaitan yan kasuwa.
An kirki wannan hukumar karkashin dokar samar da aiki ta shekarar 2022, wanda aka sanyawa hannu a watan disembar shekarar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: