Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, a jiya Litinin, ya bayyana cewa a zaman majalissa na karshe a wannan makon zasu amince da kasafin kudi na 2022 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar.
Ahmad Lawan ya bayyana hakan ne a cikin wata makala da aka gabatar a jerin lakcocin ‘yan majalisa na farko da cibiyar nazarin harkokin dokoki da dimokuradiyya ta kasa ta shirya.
Sanatan ya kara da cewa, albashin Sanata a duk wata Naira miliyan 1.5 ne yayin da na dan majalisar wakilai ya kai Naira miliyan 1.3
A cewar Ahmad Lawan kudaden da ake warewa majalissun kasar nan yayi kadan idan aka kwatanta da shekaru 4 da suka gabata.
Wannan na zuwa ne kimanin watanni 2 bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudi na 2022, mai kunshe da kimanin nairaTrillion 16.39, wanda yayi masa take da kasafin kudin farfado da tattalin arzikin kasa.