Majalissar dokokin jihar Jigawa ta tantance masu kula da hukumar lura da alamurran sharia ta jihar

0 235

Majalissar dokokin jihar Jigawa ta tantance tare da tabbatar da sunayen Jamila Farouk da kuma Dr Abdulkadir Sale Kazaure a matsayin wakilai a hukumar lura da alamurran sharia ta jiha

A lokacin tantancewar, yan majalissun dokokin jiha masu wakiltar mazabar Kanya da Sule Tankarkar da Garki sun yi tambayoyi tare da nuna gamsuwa da zabar mutanen biyu

Shugaban majalissar Alhaji Idiris Garba Jahun ya sanar da hakan a zaman majalissar na wannan rana inda ya bukaci sabbin wakilan hukumar dasu yi aiki tukuru domin kawo sauyi a bangaren sharia

Da yake jawabi ga manema labarai bayan an tabbatar das hi, Dr Abdulkadir Sale Kazaure ya bada tabbacin yin aiki tukuru domin kawo sauyi da cigaba a bangaren sharia

Ya kuma bada tabbacin ganin an dauki maaikatan sharia da suka dace aiki domin samun kwarewa

Haka zalika majalissar ta karbi bakuncin wakilan hukumar rabon arzikin kasa karkashin jagorancin kwamishinan hukumar na kasa Alhaji Ahmed Mahmud

Alhaji Ahmed Mahmud yace sun ziyarci majalissar ne domin neman shawarwari kan batun samar da sabon tsarin rabon arzikin kasa. A nasa jawabin shugaban majalissar Alhaji Idris Garba Jahun ya bada tabbacin majalissar na yin dukkannin abin da ya dace domin samun nasarar aiyukan hukumar

Leave a Reply

%d bloggers like this: