Majalissar masarautar Gumel ta bada sabuwar motar sintiri ga ofishin shiyyar Gumel na hukumar NDLEA domin gudanar da aiyukanta

0 67

Majalissar masarautar Gumel ta bada sabuwar motar sintiri ga ofishin shiyyar Gumel na hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) domin gudanar da aiyukanta.

Mai martaba sarkin Gumel Alhaji Ahmed Muhammad Sani ta hannun Galadiman Gumel Alhaji Usman Maje Muhammad ya mika makullan motar ga sakataren kwamitin yaki da badala na masarautar Alhaji Salisu Mazge.

Mai martaba sarki ya bukaci hukumar da ta yi cikakken amfani da motar wajen kawo karshen aiyukan masu taamali da miyagun kwayoyi a kananan hukumomin masarautar.

A nasa jawabin kwamandan hukumar yaki da taamali da miyagun kwayoyi na kasa, Kingsley Effiong, ya yabawa masarautar Gumel bisa wannan karamci tare alkawarin yin cikakken amfani da motar wajen yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi a masarautar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: