Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo zai kaddamar da cibiyar kula da kanana da matsakaitan yan kasuwa, karo na 28, a Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai bawa gwamna shawara na musamman akan kafafen yada labarai da huldar jama’a, Habibu Nuhu Kila, wacce ya rabawa manema labarai.

Sanarwar ta kara da cewa mataimakin shugaban kasar zai kuma kaddamar da titin gwamnatin tarayya mai tsayin kilomita 40 a jihar tare da raba kayayyakin tallafi.

Kamar yadda yazo a sanarwar, za a tarbi mataimakin shugaban kasar a filin jiragen saman kasa da kasa na Dutse da misalin karfe 11 na safe.

An shirya tsara gudanar da abubuwan a dakin taro na Ahmadu Bello domin kaddamar da cibiyar kula da kanana da matsakaitan yan kasuwa, dandalin taro na Aminu Kano Triangle domin raba kayan tallafi da kuma mahadar gidan man NNPC domin kaddamar da titunan, duka a birnin Dutse.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: