Dalilin da yasa har yanzu gwamnatin Neja bata yi amfani da karfi ba akan wadanda suka sace daliban Islamiyya ba

0 103

Sakataren gwamnatin jihar Neja, Ibrahim Matane, ya bayyana dalilin da yasa har yanzu gwamnatin jihar bata yi amfani da karfi ba akan wadanda suka sace dalibai 138 na makarantar Islamiyyar Salihu Tanko, duk da kasancewar an san inda suke.

Ibrahim Matane yace gwamnati na bi a sannu a hankaline domin bibiyar tattaunawar da aka yi da yan fashin dajin, da nufin magance asarar rayukan yaran.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar na duba sauran damarmakin tattaunawar wacce bata shafi biyan kudin fansa ba, kafin ayi amfani da karfi.

Da aka tambayeshi dangane da tattaunawar da gwamnatin ke yi da barayin, sakataren gwamnatin yace gwamnati ta gayawa yan fashin dajin cewa idan suka ajiye makamansu tare da sakin daliban, baza a hukunta su ba.

Ya kuma tabbatar da cewa maharan sun nemi iyayen yaran domin neman kudin fansa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: