Shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPC) yace kamata yayi farashin man fetur ya haura naira 280 kowace lita.

Da yake magana ta gidan talabijin na Channel, Mele Kyari yace ya kamata ace farashin litar man fetur ta haura naira 280, wanda shine farashin da ake sayar da disel a halin yanzu.

Yace gwamnatin tarayya tana cigaba da tattaunawa da kungiyar kwadago ta kasa (NLC) dangane da farashin na man fetur.

GettyImages

Yace dangane da tattaunawar da ake cigaba da yi, baza a kara farashin man ba a watan gobe na Yuli.

Mele Kyari ya kara da cewa kasancewar tallafin man fetur ba mai dorewa bane, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci NNPC da tayi duk mai yiwuwa wajen ganin cewa ‘yan Najeriya na iya sayen man fetur, musamman a wannan lokacin.

Shugaban na NNPC yace duk da kasancewar NNPC na samar da lita miliyan 60 ta man fetur a kowace rana, kamfanin bashi da tabbacin cewa ana shanye man gabadaya a cikin kasarnan.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: