Gwamnatin Tarayya ta zabi fiye da mutane dubu 13 domin basu dubu talatin-talatin a Jigawa

0 104

Gwamnatin Tarayya ta zabi mutane marasa karfi dubu 13 da 912 domin a basu naira dubu talatin-talatin a karkashin shirin tallafi, a jihar Jigawa.

Jagoran shirin na jihar Jigawa, Mustapha Umar, ya sanar da haka a lokacin wata ganawa da kungiyoyin fararen hula da ‘yan jarida.

Yayi bayanin cewa an fito da shirin ne domin zakulo mutanen da annobar corona ta ruguza tattalin arzikinsu.

FACEBOOK/NSIP

Mustapha Umar yayi nuni da cewa gwamnatin tarayya ta zabi wadanda za suci gajiyar shirin daga al’umomi 535 da mazuban siyasa 12 a kananan hukumomin 8 na jihar.

Yace duk wanda aka zaba zai samu jumillar naira dubu talatin cikin watanni 6, inda ya kara da cewa kananan hukumomin sune Babura da Birniwa da Kafin Hausa da Gwaram da Jahun da Hadejia da Dutse da kuma Malam Madori.

Leave a Reply

%d bloggers like this: