MDD Ta Musanta Sakataren Majalisar Antonio Gutterres Yana Kaffa-kaffa Da Kasar Rasha.

0 71

Majalisar Ɗinkin Duniya ta sa ƙafa ta shure rahotannin da ke cewa babban sakataren majalisar Antonio Gutterres yana kaffa-kaffa da kasar  Rasha.

Wasu takardu da gwamnatin Amurka ta bankaɗo sun nuna cewa jami’an na Amurka sun yi amannar cewa a shirye Guteress yake ya haɗa kai da wasu kamfanoni da ke ƙarƙashin takunkuman ƙasashen yamma domin samun damar fitar da hatsi da kuma taƙi zuwa ƙasashen Afrika da kuma Asiya. Wani babban jami’in MDD ya ce Mr. gutteress na bukatar a saukakawa kasashe marasa karfi ne kawai radadin yakin Russia da Ukraine.

Leave a Reply

%d bloggers like this: