Zababbun Yan Majalisar Dattawa Sun Fara Takarar Neman Kujerar Shugaban Majalisar

0 121

Gabanin kaddamar da majalisar dokokin kasarnan karo na 10, zababbun ‘yan majalisar sun fara takarar neman kujerar shugaban majalisar dattawa.

Za a bude majalisar ta 10 ne a watan Yunin 2023 bayan rantsar da zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.

A cikin majalisar, majalisar ta 10 za ta kasance da ‘yan majalisar wakilai daga jam’iyyar APC, PDP, Lb Party, da NNPP,Sauran sun hada da SDP, APGA da YPPP.

Yayin da APC ta samu kujeru 57, PDP ta samu kujeru 29, jam’iyyar Labour ta koma gida da kujeru 6. Sauran sun hada da NNPP da SDP mai mambobi 2 kowannensu, yayin da APGA da YPPP ke da mambobi daya.

Baya ga shugabancin majalisar dattawa, akwai mukamai kamar mataimakin shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai.

Shugabanni masu rinjaye da marasa rinjaye, mataimakin shugaban masu rinjaye, masu rinjaye ko babban mai tsawatar, mataimakin mai tsawatar, shugaban marasa rinjaye, mataimakin shugaban marasa rinjaye da dai saurancu.

Sai dai an fara fafatawa a zaben shugaban majalisar dattawa tun kafin kaddamar da ‘yan majalisar wakilai ta 10. Ana rade-radin cewa zaben shugaban majalisar dattawan zai ta’allaka ne kan yadda jam’iyyar APC mai mulki ta ware ofishin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: