Ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo ya roki yan najeriya da su nuna halin dattako da kishin kasa tare da baiwa shugaban kasa Bola Tinubu karin lokaci domin cimma manufofin tattalin arziki masu dogon zango daya tsaro.
Ministan wanda ya kasance bako a wani shirin gidan talabijin na Channels, ya bukaci masu shirin su kasance masu kishin kasa.
Yace bai kamata a hakunta Tinubu ba kan tsammanin warware matsalolin kasar nan 100/100 cikin shekara guda.
Yace ba’a gina tattalin arziki dare daya, halin da ake ciki a yanzu jumillar zunubin shekaru 60 ne na rashin iya jagoranci.