Peter Obi ya bayyana cikekken goyon bayansa kan zanga-zangar da za’ayi a watan Agusta
Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar Labour a zaben daya gabata Peter Obi, ya bayyana cikekken goyon bayansa kan zanga-zangar kasa da aka shirya gudanarwa a watan Agusta.
Obi wanda kuma tsohon gwamnan jihar Anambra ne, yace kundin tsarin mulkin kasa ne ya bada damar gudanar da zanga-zanga a matsayin yancin da yan kasa ke dashi.
Sai dai yayi gargadi kan tayar da hatsaniya, yana mai cewa ya zama wajibi a gudanar da irin wannan zanga-zanga bisa tsarin doka.
Obi wanda ya ayyana Yunwa da rashin kyakkyawan fata a tysakanin matasa ne suka dauki nauyin zanga-zangar, yana mai kira ga hakumomi su bayar da kunnuwan basira wajen saurarar korafe-korafen masu zanga-zanga.
A wajen Obi babu wani aibu ga masu shiga zanga-zanga.
Jigon jam’iyyar Adawar ta Labour, ya bukaci hakumomin tsaro su tabbatar da bayar da kariya ga masu zanga-zangar, yana mai cewa suyi aiki bisa doron doka.