Ministan harkokin wajen Isra’ila Yair Lapid ya bukaci a dauki tsatstsauran mataki sakamakon harin da aka kai kan wani jirgin dakon man Isra’ilar a tekun Arabia inda biyu daga cikin mutanen da ke jirgin suka mutu.

Ma’aikatar shari’a ta Amurka ma ta bayyana damuwa kan harin da ya yi sanadin mutuwar wani dan Burtaniya da dan Romaniya.

Majiyoyi daga Amurka da Turai sun ce Iran na cikin kasashen da ake zargi da kai harin sai dai ya yi wuri a tabbatar da hakan.

Ana zargin Iran da kai hare-hare kan jiragen ruwa masu alaka da Isra’ila a watannin baya-bayan nan.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: