Mutane biyar sun mutu yayin da wasu biyu suka samu raunuka a wani hatsarin mota kirar Golf Volkswagen da Keke Napep a hanyar Kwanar Dumawa zuwa Kunya a karamar hukumar Minjibir.

Hatsarin wanda ya afku a jiya, ya shafi fasinjojin da ke tafiya zuwa kauyukan da ke kusa.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kwamandan shiyya na hukumar kiyaye haddura ta kasa, Zubairu Mato, ya ce hatsarin ya faru ne sakamakon gudun wuce gona da iri.

Ya ce mutanen biyar da suka hada da maza hudu da mace daya sun rasa rayukansu yayin da biyun da suka samu raunuka duka maza ne.

A cewarsa, bayan samun rahoton aukuwar hatsarin, tawagarsa a ofishin Minjibir ta isa wajen da lamarin ya auku inda suka kai wadanda suka jikkata zuwa manyan asibitocin Minjibir da Dambatta kuma likita ya tabbatar da mutuwar mutane biyar.

Ya kara da cewa mutanen biyu da suka jikkata a halin yanzu suna samun kulawa a asibiti.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: