Wata Kotu ta bayar da umarnin tsare wani a gidan yari bisa zarginsa da bata sunan Gwamnan Jihar Kano

0 70

Wata Kotun Majistare a Jihar Kano da ke zaman a Nomansland ta bayar da umarnin tsare wani mai suna Mu’azu Magaji Danbala a gidan yari bisa zarginsa da bata sunan Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

An tuhumi wanda ake zargin da yin kalaman batanci ga gwamnan da ‘ya’yansa biyu; Abdul’aziz da Balaraba, a shafin Facebook.

Daya mutumin da ake tuhuma mai suna Jamilu Shehu, ba a same shi ba har yanzu.

An gurfanar da mutanen biyu a gaban kuliya bisa zargin hadin baki domin cin zarafi da tada hankalin jama’a da bata sunan wasu, laifukan da suka sabawa wasu sassan kundin manyan laifuffuka.

A cewar rahoton farko a ranar 26 ga Oktoba, 2021, shugaban karamar hukumar Nassarawa, Auwal Lawal Shuaibu, ya kai korafi ga hukumar leken asiri ta musamman ta jihar Kano, inda yake karar mutanen biyu mazauna Sabon Garin Kiru da ke karamar hukumar Kiru ta jihar Kano.

Sai dai wanda ake zargin ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, sannan lauyan wanda ake zargin ya nemi a ba shi belinsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: