An kashe mutane uku tare da jikkata wasu da dama a jiya a karamar hukumar Offa da ke jihar Kwara yayin da wasu ‘yan daba suka yi arangama bayan da aka samu rashin jituwa kan wata budurwa.

An gano cewa lamarin ya fara ne da daren ranar Asabar.

Wani mazaunin garin, Alhaji Abdulrahman, ya shaida wa manema labarai cewa rikicin ya faru ne tsakanin ’yan uwa Isale Oja da Oja Oba na garin Offa.

A cewarsa, an fara samun rikicin ne bayan daya daga cikin shugabannin kungiyar ya sace budurwar wani dan kungiyar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da mutuwar ‘yan fashin guda biyu, inda ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike akan lamarin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: