Jami’an tsaron Saudiyya da ke birnin Makkah sun kama wasu mazauna birnin da wadanda suka kama suna bara an kuma kama biyu a kusa da masallacin Ka’aba.

Hukumomin sun ce sun kama wani dan kasar Indiya saboda an kama shi yaa kokarin karkatar da hanulan masu ibada domi su ba shi kudi, sannan sun damke wani dan asalin kasar Moroko da yake bara a jikin wata kofar shiga masallacin Ka’aba.

Akwai kuma wani dan kasar Yemen wanda ke amfani da sandunan guragu domin yaudarar masu ibada cewa shi mai nakasa ne.

Kana an kama wani mutum da ke tura dansa ya yi bara ta hanyar saka shi a kan keken guragu. Bincike ya tabbatar cewa dan nasa kalau yake.

Hukumar da ke kula da tsaron al’umma ta Saudiyya ta sanar cewa duk wanda aka kama yana bara, ko kuma wanda ya iza wani ya yi bara, ko ma ya amince da yin barar – zai shafe kusan shekara guda yana zaman gidan kaso ko ya biya tarar Riyal 100,000 ko ma duka.

BBCHausa

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: