Mutum 50 sunci gajiyar horon aikin jarida na zamani da tantance gaskiya wanda hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa (NITDA) ta yi a jihar Jigawa

0 77

A cigaba da kokarinta na bunkasa kwazon ma’aikatan yada labarai a kasarnan, akalla ‘yan jarida da masu fada a ji a kafafen sadarwa na zamani 50 ne suka ci gajiyar horon aikin jarida na zamani da tantance gaskiya wanda hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa (NITDA) ta dauki nauyi.

Horon wanda kamfanin dake wallafa jaridar PRNigeria tare da tallafin NITDA suka shirya ya gudana ne a cibiyar Manpower dake Dutse.

Horon ya koyawa mahalarta dabaru daban-daban da suka hada da da’ar watsa labarai, aikin jarida na zamani da tabbatar da sahihancin labarai, da sauransu.

A yayin da take bayyana bude taron, shugabar sashen wayar da kai ta NITDA, Hadiza Umar ta bayyana cewa taron karawa juna ilimin na daya daga cikin muhimman ayyuka da manufofin hukumar da nufin baiwa ‘yan jarida ilimi da dabarun aikin jarida na zamani.

Kafin mikawa mahalarta taron satifiket, mai baiwa gwamnan jihar Jigawa shawara kan harkokin yada labarai Habib Kila ya yabawa hukumar NITDA bisa ayyukan fasaha da shirye-shiryenta na bunkasa fasahar zamani a fadin kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: