Asusun Kula da Ƙananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya Unicef ya ce Najeriya ta yi asarar dala biliyan 100 sakamakon yaƙin da ake yi a yankin arewa maso gabashin ƙasar.
Cikin wani sabon bincike da Asusun ya gudanar ya yi gargaɗin cewa lokaci ya yi da muhukunta za su ɗauki mataki, saboda yadda rayuwar ƙananan yara ke cikin barazana.
Binciken ya ce kusan yara miliyan ɗaya ne ba sa zuwa makaranta a yankin sakamakon rikicin ‘yan bindiga da yankin ke fama da shi.
Unicef ya kuma nuna yadda rikicin ya ƙara ta’azzara tattalin arzikin ƙasar, lamarin da asusun ya ce na barazana ga rayuwar miliyoyin ƙananan yara ga ƙasar baki-ɗaya. A cewar rahoton binciken illar yaƙi ba ta tsayawa ga yankin da ake gwabza yaƙin kaɗai ba. Duka Najeriya na ji a jikinta sakamakon yakin da ake yi a yankin, tattalin arzikinta ya samu cikas sakamkon wanna rikici”