Najeriya za ta karbi bashin dala biliyan 1.57 daga Bankin Duniya

0 83

Bankin Duniya ya amince da kashe kuɗi dala biliyan 1.57 domin tallafa wa gwamnatin Najeriya wajen inganta ayyukan kyautata rayuwar ‘yan ƙasa, da yaƙi da sauyin yanayi, da lafiyar mata.

Za a kashe kuɗin ne a mataki uku kan abubuwan da suka haɗa da rage aukuwar bala’i kamar ambaliya da fari ta hanyar inganta lafiyar madatsun ruwa a ƙasar, da kuma noman rani.

Sabon ƙunshin tallafin ya kuma ƙunshi dala miliyan 500 na kyautata harkar koyo da koyarwa da lafiya, da miliyan 570 na inganta cibiyoyin lafiya a matakin farko, da kuma miliyan 500 na samar da lantarki mai ɗorewa da noman rani a Najeriya.

Ana sa ran ɓangaren ilimi da na lafiya a matakin farko za su amfana ta hanyar kyautata ayyuka, da ɗaukar ma’aikata.

Kazalika, ana sa ran ‘yan Najeriya 950,000 za su amfana da tallafin ta hanyar noman rani da ba shi da matsala ga muhalli.

Leave a Reply

%d bloggers like this: