An samar da dakunan shan maganin dabbobi na tafi da gidanka guda 535 a jihar Jigawa

0 81

Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da dakunan shan magani na tafi da gidanka, da nufin samar da ayyukan kiwon lafiyar dabbobi kyauta a fadin kananan hukumomi 27 na jihar Jigawa.

Shirin dai shi ne na farko a Jigawa, inda ya yi daidai da ajandar gwamnati mai dauke da abubuwa 12 na inganta rayuwar mazauna yankin musamman a yankunan karkara da makiyaya.

Yayin kaddamar da shirin a kauyen Garbau da ke karamar hukumar Miga, Gwamna Namadi ya jaddada muhimmancin shirin ga tattalin arzikin jihar, musamman ga Fulani makiyaya da suka dogara da kiwo.

Gwamna Namadi ya sanar da cewa kowace karamar hukuma za ta samu cikakkun ingantattun babura guda biyar domin gudanar da aikin kula da lafiyar dabbobi, wanda ya kai jimillar 535 na asibitocin tafi da gidanka  a fadin jihar.

Gwamnan Ya kuma jaddada muhimmancin tabbatar da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya ta hanyar kiyaye hanyoyin shanu, da inganta wuraren kiwo, da tabbatar da samun ruwa ta ingantattun magudanan shayarwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: